30 Satumba 2021 - 13:11
​A Karon Farko Bayan Fitowarsa Daga Gidan Yari Sheikh Ibrahim El-Zakzaky Ya Yi Hira Da Tashar Presstv

Shugaban harkar Musulunci ko IMN ta ‘yan shi’a a tarayyar Najeriya Sheikh Ibrahim El-Zakzaki ya yi hira da tashar talabijin ta Presstv mai watsa shirye-shiryensa da harshe turanci a nan Tehran.

Bayan tsare shi na shekaru 6, kimani watanni biyu kenan da wata kotu a birnin kaduna ta wanke shugaban kungiyar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (s) ta IMN Shekh Ibrahim El-Zakzaki tare da matarsa Malama Zanit daga dukkan laifuffukan da ake tuhumarsu.

An kama shugaban na IMN ne a shekara ta 2015 bayan da sojojin Najeriya suka kashe da dama daga cikin mabiyansa daga ciki har da ‘yayansa 3 a gidansa dake birnin Zariya na jihar Kaduna. Banda haka sojojin sun lalata duk abinda suka mallaka a gidan. Sannan suka kamsu shi da wasu da dama daga cikin mabiyansa suka tsare.

A hirar ta farko da ta hada shi da tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran Sheikh Zakzaki ya bayyana hakikanin abinda ya faru da shi da magoya bayansa a cikin watan Decembar shekara ta 2015. Ya kuma kara da cewa, al-amarin wata jarrabawar Allah ta’ala ce, kuma ko kaden ba zai hana shi da mabiyansa ci gaba kan tafarkin da suke kai ba.

Malamin ya bayyana cewa a halin yanzu da shi da matarsa suna bukatar zuwa ganin likita a kasashen wajen saboda jinya,amma hukumomin a kasar sun ki bada wannan damar.

342/